Hukumar Kula da Dabbobin ta Namibia ta sanar da barkewar cutar dawakan Afirka, tare da tabbatar da bullar cutar guda 25 a gundumomin dabbobi na jihar Otjinene, Windhoek, Okahandja, Omaruru, Gobabis, da Mariental.
Mukaddashin babban jami’in kula da dabbobi, Johannes Shoopala ya ce, ya fitsr ds sanarwar s ranar Juma’a Da Ta gabata, ce wa hukumomi sun aiwatar da matakan dakile yaduwar cutar cikin gaggawa.
“Matakin sun hada da neman izinin likitan dabbobi da cikakken allurar rigakafi ga dabbobi masu shiga da komuwa Daga wuraren da abin ya shafa, ba da shawara ga masu su da su yi wa dabbobinsu allurar, Ko a keɓe wuraren da abin ya shafa, ba da shawarar tsagaita Ko dare da amfani da maganin kwari, hana tseren dawakai, shigo da kayayyaki daga ƙasashen da suka kamu da cutar, da tunatar da jama’a game da buƙatun izinin motsi,” in ji shi.
A cewar Shoopala, lokacin da aka ba da shawarar yin rigakafin a Namibiya daga 1 ga Yuni zuwa 31 ga Oktoba.
An siffanta cutar dawakai na Afirka a matsayin cuta mai saurin yaduwa ta hanyar tsaka-tsaki da ke shafar dawakai, jakuna, zebra, da sauran nau’in equine.
Alamomin cutar da aka saba, sun hada da zazzabi, numfashi, tari, gumi, da fitar kumfa daga hanci; Yawan mace-macen zai iya kaiwa kashi 70.
Xinhua/Aisha.Yahaya, Lagos